Saudiyya Ta Yanke Taimakon Da Take Bai Wa Palasdinawa
Oct 26, 2016 02:59 UTC
Koma Bayan Tattalin Arzikin Saudiyya Ya Sa Ta Yanke Taimako Ga Palasdinawa.
Kamfanin Dillancin Labarun Palasdinu na " Sama" ya ambato jami'an gwamnatin Palasdinu na cewa: Watanni shida ajere kenan Saudiyya ba ta basu taimakon dala 20 da ta saba bayarwa a kowane wata ba.
Majiyar Palasdinun ta ce har yanzu ba ta sami wani cikakken bayani ba daga Saudiyya din akan dalilin yanke bata tallafin na wata-wata.
Kasar Saudiyyar dai tana fuskantar koma bayan tattalin arziki, wanda ya samo asali daga faduwar farashin man fetur da ta taka rawa wajen rage shi a karshen 2014.
Tags