An kashe wata Mata a gidan yari saudiya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i13021-an_kashe_wata_mata_a_gidan_yari_saudiya
Wata Mata 'yar kasar Saudiya ta rasa ranta a gidan Yari sanadiyar bakar azabar da ta fuskanta
(last modified 2018-08-22T06:59:09+00:00 )
Oct 27, 2016 14:36 UTC
  • An kashe wata Mata a gidan yari saudiya

Wata Mata 'yar kasar Saudiya ta rasa ranta a gidan Yari sanadiyar bakar azabar da ta fuskanta

A wata fira da tashar telbijin din Press tv tayi da Ali Al-Ahmad mai rajin kare hakin bil-adama kuma shugaban cibiyar dake kula da al'amuran yankin tekun Fasha dake birnin Watsinton na kasar Amurka ya ce Matar mai suna Hanan Alzabyani ta rasa ranta ne a gidan yarin garin Jedda sanadiyar bakar azabar da ta fuskanta daga Jami'an tsaron gidan yarin.

Al-Ahmad ya tabbatar da cewa magabatan gidan yarin na Zahban izinin ganin fuskar mamaciyar kawai suka baiwa iyayenta, daga bisani suka bisne gawarta a wani boyayyen wuri da ma'aifanta ba su sani ba.sannan kuma a tilasta musu sanya hannu kan takardar cewa 'yarta su wa'adinta ne ya yi ta cika ba wai sanadiyar azabtar da ita ba ne ,ta yadda nan gaba babu wani da zai tuhumi magabatan gidan yarin.

Magabatan kasar Saudiya ne sun jima suna fuskantar kakkausar suka tare da alawadai daga kungiyoyin kare hakin bil-adama na kasa da kasa game da yadda suke rusa masu adawar da siyasar su gami da yi musu bakar azaba har ta kai ga rasa rayuka.