Saudiyya : An Dakile Yunkurin Kai Hari A Jeddah
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i13138-saudiyya_an_dakile_yunkurin_kai_hari_a_jeddah
Hukumomi a Saudiyya sun sanar da dakile wani yunkurin kai wani hari da aka shirya kaiwa a filin wasa na birnin Jeddah dake yammacin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:59:09+00:00 )
Oct 30, 2016 11:02 UTC
  • Saudiyya : An Dakile Yunkurin Kai Hari A Jeddah

Hukumomi a Saudiyya sun sanar da dakile wani yunkurin kai wani hari da aka shirya kaiwa a filin wasa na birnin Jeddah dake yammacin kasar.

Wata sanarwa daga ma'aikatar cikin gidan kasar ta ce an gano wasu wurare biyu inda 'yan ta'addan IS ke shirya kai hari a cikin kasar.

Sanarwar ta ce anyi nasara cafke mutane hudu- hudu a cibiyoyin da suke shirya yadda zasu kai hare-haren. 

kakakin ma'aikatar harkokin cikin gina na kasar ya ce cibiyar 'yan ta'addan t afarko an gano ta ne a lardin Chaqra dake arewa maso yammacin kasar kuma dukkan 'yan ta'addan 'yan asalin kasar ta Saudiyya ne wadanda ke samun umurni daga wani kwamandan kungiyar ta Da'esh tun daga Syria kuma suna shirya kai hari kan jami'an tsaron kasar.

A cibiyar 'yan ta'addan ta biyu inda 'yan ta'addan ke shirya kai hari a filin wasa na Jeddah nan ma an cafke mutane hudu da suka hada da 'yan asalin Pakistan biyu, Da san Syria da kuma dan Saudiyya guda.

Tun a shekara 2014 ne Saudiyya ta fara fuskantar hare-hare 'yan ta'adda wadanda galibi kungiyar IS ke daukan alhakin kaiwa.