Palasdinu: Wani Matashin Bapalasdine Ya yi Shahada A yau juma'a.
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i14083-palasdinu_wani_matashin_bapalasdine_ya_yi_shahada_a_yau_juma'a.
Yahudawan Sahayoniya Sun Kashe wani Bapalasdine
(last modified 2018-08-22T11:29:16+00:00 )
Nov 18, 2016 19:02 UTC
  • Palasdinu: Wani Matashin Bapalasdine Ya yi Shahada A yau juma'a.

Yahudawan Sahayoniya Sun Kashe wani Bapalasdine

Wani matashin Bapalasdine guda ya yi shahada a yankin Gasa a yau juma'a.

Kakakin ma'aikatar kiwon lafiya, Ashraf Qudwa, ya ce; Sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila, sun kai hari a sansanin 'yan gudun hijira na al-Buraij, da ke Gaza, inda su ka kashe wani matashi dan shekaru 26.

A cikin kwanaki biyu da su ka gabata ma dai, sojojin na 'yan sahayoniya sun kai wani harin a wannan sansanin na al-buraiji, tare da jikkata palasdinawa biyu.

A watan Oktoba kadai, sojojin haramtacciyar Kasar Amurka, sun kame palasdinawa 554 a cikin yankuna daban-daban na yammacin kogin jordan.