Shugaban Turkiyya Ya Fara Ziyara Kwanaki Biyar A Afirka
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i1444-shugaban_turkiyya_ya_fara_ziyara_kwanaki_biyar_a_afirka
Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya isa kasar Ivricos jiya Lahadi a ziyarar kwanaki biyar daya fara a nahiyar Afirka.
(last modified 2018-08-22T11:27:53+00:00 )
Feb 29, 2016 06:15 UTC
  • Shugaban Turkiyya Ya Fara Ziyara Kwanaki Biyar A Afirka

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya isa kasar Ivricos jiya Lahadi a ziyarar kwanaki biyar daya fara a nahiyar Afirka.

Bayan ziyara da ya kai bara a gabashin Afirka da kuma Senegal a watan Janairu, a wannan karo shugaba Erdogan zai ziyarci wasu kasashe hudu na kungiyar ECOWAS.

Wannan ziyara dai nada zumar kara dangantaka da kasuwanci da zuba jari a wannan nahiyar, a daidai lokacin da kasar ta Turkiyya ke fuskantar tarin matsaloli tsakanin ta da makoftan ta.

A wannan ran-gadi da Mr Erdogan ya fara da Cote d'ivoire, zai kuma isa kasashen Ghana, Najeriya da kuma Guinea a daidai lokacin da kasashen Turai da China ke ci gaba da mamaye harkokin kasuwanci dama fadada harkokin su a wannan nahiyar.

Kiyasi ya nuna cewa tun daga shekara ta 2009 Turkiyya ta ninka adadin ofisoshin jakadancin dama fadada zirga-zirga kanfanin jirgin saman ta na Turkish air a wannan nahiyar ta Afirka.