Masar: An dauke makasan Sheikh Shahata Shekaru 14 A gidan Kurkuku.
Dec 08, 2016 12:22 UTC
An Yanke hukuncin zaman kaso na shekaru masu yawa ga makasan malamin shi'a a Masar.
Kuton laifuna a kasar Masar ta yanke hukuncin zaman kisa ga mutanen da suke da hannu a kashe malamin shi'ar kasar, Sheikh Hassan Shahata da makusnatansa uku.
Kotun ta yanke zaman kurkuku na shekaru 14 akan Ahmad al-Akhras, wanda shi ne abin tuhuma na farko, a kisan gillar da aka yi wa sheikh Hassan Shahata.
A cikin watan yuni na 2013 ne wasu 'yan salafiyya masu tsattsauran ra'ayi a kasar Masar su ka jagoranci kashe Sheikh Hassan Shahata a kauyen Abu Muslim.
kauyen na Abu Muslim wanda ya ke a gundunar al-jizah, yana daga cikin cibiyoyin mabiya mazhabar shi'a.
Tags