Masar: Karuwar Adadin Wadanda Su ka Rasa Rayukansu A Harin Alqahira.
Dec 11, 2016 19:08 UTC
Harin Ta'addanci A Kasar Masar
Ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Masar, ta sanar da cewa; Adadin wadanda su ka rasa rayukansu sanadin harin ta'addancin da aka kai a wata majami'a a birnin alqahira sun karu zuwa 20.
Ma'aikatar kiwon lafiyar ta Masar ta ci gaba da cewa; A halin da ake ciki a yanzu ana bada taimakon da ya dace ga wadanda su ka jakkata a sanadin harin.
Da safiyar yau ne dai aka sanar da tashin wasu abubuwa a cikin majami'ar Saint Marck da ke unguwar Abbasiyya a cikin birnin alqahira. Sanarwar farko ta ce mutane biyar ne su ka kwanta dama.
Masar ta fada cikin matsalolin tsaro tun faduwar gwamnatin Muhammadu Mursi a 2013.
Tags