Sakon murna na Shugaba Asad dangane da 'yanta Aleppo
Shugaban Kasar Siriya ya yi Al'ummar kasar murna da 'yanto garin Aleppo
Yayin da ake ci gaba da kwashe 'yan ta'adda daga gabashin birnin Aleppo, Shugaban kasar Siriya Bashar Al-assad cikin wani sakon vidio da aka watsa a gidajen telbijin din kasar ya taya Al'ummar kasar murna kan gagarumar nasarar da Sojojin kasar suka samu na 'yanto garin Aleppo tare da bayyana cewa wannan nasara babban tarihi ce ga Al'ummar kasar Siriya gaba daya.
Shugaba Assad ya kara da cewa abinda ya wakana yanzu a birnin Aleppo na arewacin kasar, sakamakon kokari , jajircewa da kuma aiki tare na Al'ummar kasar ne, kuma wannan nasara da aka samu na 'yanto garin Aleppo ba wai kawai yanayin Siriya da kuma yankin ba ne kawai ya canza, zai samar da daidaito a Siyasar Duniya gaba daya.
A cikin watanin da suka gabata birnin Aleppo dake a matsayin babban birni na biyu a kasar Siriya ya fuskanci gumurzu mai tsanani tsakakin kungiyoyin 'yan t'adda da Dakarun tsaron kasar, a daren Talatar da ta gabata ce Dakarun Siriyan suka samu nasarar 'yanto garin baki daya daga mamayar 'yan tawaye da kuma kungiyoyin 'yan ta'adda.