Shirin Kungiyar Agaji na fitar da fararen hula daga birnin Aleppo
Kakakin Kwamitin kasa da kasa na kungiyar kai Agajin gaggawa ya bayyana fatansa na gaggauta ci gaba da aiyukan fitar da fararen hula gami da wadanda suka ji rauni daga gabashin birnin Aleppo
Kamfanin dillancin Labaran Reuteus ya nakalto Elodie Schindler Kakakin Kwamitin kasa da kasa na kungiyar kai Agajin gaggawa, yayin da yake zantawa da manema labarai na cewa, kungiyar su a shirye take wajen ci gaba da fitar da fararen hula gami da wadanda suka jikkata daga gabashin birnin Aleppo.
A jiya Assabar ma kungiyar kai Agajin gaggauwa ta bukaci kungiyoyin 'yan ta'adda da suke ci gaba da garkuwa da fararen hula da su mutunta yarjejjeniyar da aka cimma su kuma gaggauta bari a ci gaba da aiyukan fitar da fararen hula daga gabashin birnin na Aleppo tare da bada tabbaci na lafiyar su.
Rahotanni daga birnin Siriya na nuni da cewa Dubban farar-hular da aka rutsa da su a birinin Aleppo ke cikin mawuyacin hali a yayin da ake jan-kafa wajen aiwatar da yarjejeniyar da gwamnati da 'yan tawaye suka kulla ta kwashe su daga birnin, inda wani gungu na 'yan ta'adda ke ci gaba da jan kafa wajen aiwatar da wannan yarjejjeniya bayan da Dakarun Gwamnati suka hana su fita da makamai da kuma milyoyin Dalolin Amurka daga cikin birnin.