An Kashe Jakadan Kasar Rasha A Birnin Ankara Na Kasar Turkia
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i15469-an_kashe_jakadan_kasar_rasha_a_birnin_ankara_na_kasar_turkia
Rahotannin da suke fitowa daga kasar Turkia a dazo dazon nan sun nuna cewa Jakadan kasar Rasha a birnin Ankara na kasar Turkia ya ji mummunan raunuka bayan an harbe shi da bindiga a yau Litinin.
(last modified 2019-03-07T02:07:59+00:00 )
Dec 19, 2016 14:14 UTC
  • An Kashe Jakadan Kasar Rasha A Birnin Ankara Na Kasar Turkia

Rahotannin da suke fitowa daga kasar Turkia a dazo dazon nan sun nuna cewa Jakadan kasar Rasha a birnin Ankara na kasar Turkia ya ji mummunan raunuka bayan an harbe shi da bindiga a yau Litinin.

Tashar television ta Presstv a nan Tehran ta bada labarin cewa an harbi Jakada Andrey Karlov ne a lokacinda yake ziyartar wani bajekolin kayakin aikin hannu a birnin Ankara a yammacin yau Litinin a lokacinda wasu yan bindiga suka bindige shi, inda a halin yanzu yana jinya a wani asbiti a birnin. 

Tashar Television ta NTV ta kasar Turkia da kuma CNN -da harshen turkanci sun bayyana cewa jakadan ya ji mummunan raunuka kuma an ji karin harbe harbe a wurin da aka harbe shi bayan wani lokaci.

A bangaren gwamnatin Rasha dai ta tabbatar da cewa Jakadan kasar a Turkia Andrey Karlov ya rasu sanadiyar harbin da wani dan bingida yayi masa a lokacinda yake jawabi a wani taron aikin hannu a abirnin Ankara, kuma wanada ya kashe shin ya bayyana cewa wannan shi ne sakamakon abinda Rasha ta yi a halab na kasar Siria.