Netanyahu: Obama Ya Bada wa Isra'ila Kasa A Fuska
(last modified Sun, 25 Dec 2016 05:52:18 GMT )
Dec 25, 2016 05:52 UTC
  • Netanyahu: Obama Ya Bada wa Isra'ila Kasa A Fuska

Firayi ministan haramtacciyar kasar Isra'ila Benyamin Netanyahu ya yi kakkausar suka a kan shugaban kasar Amurka mai barin gado Barack Obama, kan abin da ya kira gazawar Amurka a kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya wajen kare Isra'ila.

Tashar Press TV ta bayar da rahoton cewa, ofishin Netanyahu ya fitar da wani bayani a jiya, wanda a cikinsa yake bayyana cewa, gwamnatin Obama ba kawai ta kasa kare Isra'ila ba ne a kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya, ta hada kai ne ma da sauran kasashe masu adawa da Isra'ila domin fitar da kudiri da ke yin Allawadai da ita.

Netanyahu ya ce Obama ya kasa kiyaye dadadden alkawalin da ke tsakanin Amurka da Isra'ila, na cewa Amurka za ta kare Isra'ila tare da kin amincewa da duk wani kudiri da zai soki lamirinta a majalisar dinkin duniya.

A ranar Juma'a ce kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya amince da kudirin da ke yin Allawadai da gina matsugunnan yahudawa da Isra'ila ke yi a cikin yankunan palastinawa, tare da yin kira da ta dakatar da hakan ba tare da wani bata lokaci ba.