Isra'ila Ta Gina Makeken Rami A Karkashin Masallacin Quds
(last modified Thu, 29 Dec 2016 06:59:01 GMT )
Dec 29, 2016 06:59 UTC
  • Isra'ila Ta Gina Makeken Rami A Karkashin Masallacin Quds

Ministan al’adu na Isra’ila ya ce sun gina wani ramin karkashin kasa da ya hada Wadil Hulwa da kuma Babul Magariba da ke gefen masallacin Aqsa.

Jaridar Quds Al-arabi ta bayar da rahoton cewa, ministan na Isra’ila Mary Ragif ya bayyana cewa, an kaddamar da bude wannan rami cikin nasara.

Kafin lokacin dai haramtacciyar kasar Isra’ila ta jibge darurwan ‘yan sanda a cikin kayan sarki domin tabbatar da cewa Palastinawa mazauna birnin quds ba su kawo cikas ga wannan shiri ba.

Kwamitin da ke kula da masallacin quds ya sanar da cewa tun kimanin shekaru biyu da suka gabata ne gwamnatin haramtaciyar kasar Isra’ila ta fara wannana iki, inda ta rarake bangaren kudancin masallacin aqsa da kuma gidajen Palastinawa da ke wurin, wanda a kowane lokaci wurin zai iya ruftawa, yayin da su Palastinawa da dama mazauna gabashin birnin Quds sun ce wannan fafakeken rami da Isra’ila ta haka ya cutar da gidajensu.

A cikin wannan makon ne yahudawan za su gudanar da idinsu na Hanuka, inda za su gudanar da tarukansu a cikin masallacin quds mai alfarma, tare da halartar manyan jami’an gwamnatin Netanyahu da ‘yan majalisar Kneset da sauran yahudawa masu tsatsauran ra’ayi.