Tunisiya: An Kame Daruruwan 'Yan Takfiriyya Da Su ka Koma Gida
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i15934-tunisiya_an_kame_daruruwan_'yan_takfiriyya_da_su_ka_koma_gida
Kakakin Gwamnatin Tunisiya Ya sanar da kame yan kasar da dama da su ka je jihadi kasashen waje
(last modified 2018-08-22T06:59:28+00:00 )
Dec 31, 2016 08:53 UTC
  • Tunisiya: An Kame Daruruwan 'Yan Takfiriyya Da Su ka Koma Gida

Kakakin Gwamnatin Tunisiya Ya sanar da kame yan kasar da dama da su ka je jihadi kasashen waje

Kakakin gwmanatin kasar Iyadi Damhani ya ce; Daga shekarar 2007 zuwa 2016 da ake ciki, sun kame mutane 800 da su ka dawo daga kasashen Syria da Iraki da Libya, kuma ana tsare da su a gidajen kurkuku.

Shi ma Pira ministan kasar ta Tunisiya Yusuf Shadin ya ce; Gwamnatin kasar ba ta kulla wata yarjejeniya da wata kasa ba akan komawar 'yan ta'addar kasar, kuma ba ta kare su.

Ministan harkokin cikin gidan kasar ta Tunisya ya ce; gwamnatin kasar tana da cikakken bayani akan 'yan takfiriyya 800 na kasar da su ka dawo.

Daga farkon yakin kasar Syria, dubban 'yan kasar Tunisiya ne su ke tafi kasar domin yin yaki a ciki kungiyoyin 'yan ta'adda.