Rasha Ta Fara Rage Yawan Sojojinta A Syria
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i16174-rasha_ta_fara_rage_yawan_sojojinta_a_syria
Rahotanni daga Rasha na cewa kasar ta fara rage yawan sojojinta a Syria
(last modified 2018-08-22T06:59:29+00:00 )
Jan 06, 2017 06:11 UTC
  • Rasha Ta Fara Rage Yawan Sojojinta A Syria

Rahotanni daga Rasha na cewa kasar ta fara rage yawan sojojinta a Syria

kamar yadda kafofin yada labaran kasar da dama suka rawaito babban hafsan sojin kasar, Valeri Guérassimov na fadar haka a wannan Juma'a.

Bayanai daga kasar sun ce bisa ga umurnin shugaba Vladimir Poutine, ministan tsaro kasar ya fara aiwatar da shirin kasar na rage sojin ta a kasar Syria.