Kotun Koli A Masar Tayi Watsi Da Baiwa Saudiyya Tsibirai
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i16687-kotun_koli_a_masar_tayi_watsi_da_baiwa_saudiyya_tsibirai
Kotun kolin gudanarwa a Masar tayi watsi da matakin gwamnatin Abdul fatah Al'Sisi na mallakawa masarautar Saudiyya wasu tsibiran kasar guda biyu.
(last modified 2018-08-22T06:59:33+00:00 )
Jan 16, 2017 11:53 UTC
  • Batun mikawa Saudiyya tsibiran ya janwo fishin al'umma a Masar
    Batun mikawa Saudiyya tsibiran ya janwo fishin al'umma a Masar

Kotun kolin gudanarwa a Masar tayi watsi da matakin gwamnatin Abdul fatah Al'Sisi na mallakawa masarautar Saudiyya wasu tsibiran kasar guda biyu.

A zamen data yi kotun ta ce gwamnatin kasar ba tada hurumin mallakawa Saudiyya tsibiran na Tiran da Sanafir wanda tace mallakin kasar ta Masar ne.

A watan Afrilun shekara data gabata ne gwamnatin Abdul fatah Al-Sisi ta ce ta mallakawa Saudiya tsibiran biyu, a yayin wata ziyara da sarki Salmanu ya kai a kasar, batun daya jayo kace- nace ba kadan ba tsakanin al'ummar kasar ta Masar.

Wannan matakin da kotun ta yanke a yau Litinin ya zo ne a daidai lokacin da dangantaka tsakanin kasashen biyu tayi tsami wanda a halin da ake ciki Saudiyya ta daina wadata kasar Masar din da man fetur.

Mahukuntan Alkahira da Riyad dai sun samu sabanin ra'ayi ne tun lokacin da gwamnatin Al-Sisi ta fara dasawa da gwamnatin Rasha dake goyan bayan Shugaba Bashar Al'Asad na Syria, a daidai lokacin da iata Saudiyya ke goyan bayan 'yan tawaye masu yaki da makamai.