Wani Dan Saudiyya Ya So Cinnawa Zanen Masallacin Ka'aba Wuta
Feb 07, 2017 08:49 UTC
Wani mutum dan Saudiyya da aka bayyana cewa yana fama da tabin hankali ya so cinnawa zanen dake lulube da masallacin Ka'aba mai tsarki.
Rahotanni daga Saudiyya sun ce tun da farko mutumin ya banka ma kansa man fetur ya kuma cinnawa kansa wuta kafin daga bisani ya nemi ya raba ga zanen dake lullube da masallacin Ka'aba.
Bayanai daga kasar sun ce jami'an tsaro masallacin sunyi nasara kauda barazana mutumin dan kimanin shekaru 40 kafin ya kai ga cimma manufarsa kamar yadda kakakin 'yan sanda masallacin ya samnar ga manema labarai.
'Yan sanda dai sun bayyana mutimin a matsayin mai tabin hankali, aman wasu rahotanni na daban sun ce mutimin ya yi ta kabbara irin ta 'yan ta'adda.
Tags