Sojojin Syria Sun Sake Samun Nasara Akan 'Yan Ta'adda.
Sojojin Syria Sun kwace wasu sabbin sansanoni daga hannun kungiyar Da'esh a yammacin birnin Ta'dammu a jiya talata.
Sojojin Syria Sun kwace wasu sabbin sansanoni daga hannun kungiyar Da'esh a yammacin birnin Ta'dammur a jiya talata.
Birnin Na Tadammur wanda sojojin kasar Syria su ka kwace shi daga hannun 'yan ta'adda a shekarar da ta gabata, ya sake shiga hannunsu adaidai lokacin da ake fadan kwato garin Halab.
A wani gefen sojojin na Syria sun share nakiyoyin da 'yan ta'adda su ka dasa a kauyukan al-bidhah al-sharqiyya da kuma bidha al-garbiyyah da su ke akan hanyar zuwa Ta'addar daga arewa maso gabas.
A jiya talata ma majiyar sojojin Syria ta tabbatar da cewa sojojin kasar sun sami wata nasarar tausa 'yan ta'addar a garin al-Bab, da kuma tuddan al-hawarah,mai muhimmanci.