Afirka Ta Kudu Na Ci-gaba Da Goyon Bayan Palestine (Zuma)
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i17559-afirka_ta_kudu_na_ci_gaba_da_goyon_bayan_palestine_(zuma)
Shugaba Jacob Zuma na Afrika ta Kudu ya yi Allah wadai da ci gaba da mamayar da yahudawan Isra'ila ke yiwa al'ummar Palestinu.
(last modified 2018-08-22T11:29:40+00:00 )
Feb 11, 2017 15:39 UTC
  • Afirka Ta Kudu Na Ci-gaba Da Goyon Bayan Palestine (Zuma)

Shugaba Jacob Zuma na Afrika ta Kudu ya yi Allah wadai da ci gaba da mamayar da yahudawan Isra'ila ke yiwa al'ummar Palestinu.

Mista Zuma wanda ke bayyana hakan a jawabinsa na shekara-shekara gaban majalisar dokoki kasarsa ya kuma nuna goyan bayan  Afrika ta Kudu matuka ga al'ummar Palestinu dake ci gaba da fuskantar zaluncin mahukuntan yahudawan mamaya na Isra'ila.

A cikin jawabin nasa Mista Zuma ya kuma ce, mamaya da kuma fadada matsugunnan yahudawan 'yan kama wuri zamna a yankunan Palestinu abun Allah wadai ne, kana kuma zai maida hannun agogo baya a yunkurin samar da kasashen biyu masu cin gashin kansu da aka dade ana fata.

Wannan dai ba shi ne karo ne farko ba da shugaba Zuma ke bayyana goytan bayan kasarsa ga al'ummar Palestinu, inda ko a watan Janairu yayin zagayowar cika shekaru 105 da kafuwar gidauniyyar ANC, ya bukaci al'ummar Afrika ta Kudu da su kaucewa zuwa Isra'ila a matsayin maida martani ga mamayar da takewa Palestinu.

Gwamnatin Afrika ta Kudu dai na kamanta mamayar da Isra'ila keyiwa Palestinu da mulkin wariyar launin fatar kasar na shekara 1948 zuwa 1994 a Afrika ta Kudu.

Ko baya ga hakan gwamnatin Afrika ta Kudu tayi wa wasu dokokin kasar kwaskwarima domin hana 'yan kasar dake da takardar 'yan kasa ta Isra'ila yin bautan kasa na aikin soji, da kuma kaucewa shigo da wasu kayan Isra'ila a cikin kasar.