Kasar Rasha Ta Jaddada Goyon Bayanta Ga Halattacciyar Gwamnatin Kasar Siriya
Ministan harkokin wajen kasar Rasha ya jaddada cewa: Kasarsa zata ci gaba da yaki da duk wasu ayyukan ta'addanci da suke neman kawar da halattacciyar gwamnatin Siriya.
Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov a yau Juma'a ya jaddada cewa: Kasarsa ba zata taba canja ra'ayi kan yaki da gungun 'yan ta'adda da suke kokarin kifar da halattacciyar gwamnatin Siriya karkashin shugabancin Bashar Asad ba.
Lavrov ya kara da cewa: Maimakon kasashen duniya su nemi hanyoyin rage halin kunci da tsaka mai wuya da al'ummar Siriya suka shiga ciki, amma sai wasu 'yan tsiraru suna kokarin ganin an kifar da halattacciyar gwamnatin kasar lamarin da Rasha ba zata taba laminta ba.
Tun a shekara ta 2011 kungiyoyin 'yan ta'addan kasa da kasa karkashin goyon baya da tallafin kasashen Amurka da Saudiyya gami da 'yan koransu suka lashi takwabin ganin sun kifar da halattacciyar gwamnatin Bashar Asad lamarin da ya janyo hasarar dubban daruruwan mutane tare da tilastawa wasu miliyoyi yin gudun hijira.