Ana ci Gaba Da Samun Sabani Tsakanin Saudiyya Da Masar.
Mar 07, 2017 09:21 UTC
Ministan harkokin wajen kasar Saudiyya ba zai halarci taro da takwarorinsa na Larabawa a birnin alkahira.
Ministan harkokin wajen kasar Saudiyya ba zai halarci taro da takwarorinsa na Larabawa a birnin alkahira.
Majiyar Kungiyar hadin kan kasashen larabawa ta ce abu ne mai yiyuwa jakadan Saudiyyar a kasar Masar, Ahmad Kahdan shi ne zai wakilci kasarsa a taro ba minista Adil Jubair ba.
Cibiyar labaru ta "Mada Misr" ta ce; rashin halartar taron da Adali Jubair zai yi, yana da alaka ne da rashiin jituwar da ke tsakanin Saudiyya da Masar.
Sabani a tsakanin kasashen biyu dai, yana da alaka ne da yakin Yemen da Syria da Saudiyyar ta ke goyon bayan kungiyoyin ta'addanci.
Tags