Makami Mai Linzami Ya Hallaka Sojin Saudiya
-
Wata motar jami'an tsaro Saudiyya
Ma'aikatar cikin gidan Saudiyya ta sanar da cewa wani makami mai linzami da aka harbo tun daga Yemen ya hallawa wani sojin ta guda.
Sanawra ta ci gaba da cewa an harbo makamin ne daga wani yankin Yemen inda 'yan gwagwarmaya neman sauyi na Houtsi ke rikeda
Makamin ya fada ne a sansanin sojin Dhahran na kasar ta Saudiyya a cikin daren jiya Alhamis, saidai ba tare da bayyana ko an samu wasu da suka raunana ba ko kuma irin barnar da makamin ya hadassa.
Wannan dai ba shi ne karon farko ba da jami'an tsaron Saudiyya ke rasa rasukansu ba a cikin irin wannan al'amari inda ko a watan daya gabata ma wani dan sanda Saudiyya ya rasa ransa a wannan yankin.
Wasu alkaluman na MDD sun nuna cewa kimanin mutane 7,700 galibi fararen hula ne suka rasa rayukansu, kana wasu Miliyan uku suka kauracewa muhallensu da kuma hadasa bala'in yunwa mafi muni a cikin shekaru biyu da Saudiyya ke jagorantar yakin ba gairi da dalili a kasar ta Yemen.