Kungiyar kasashen Larabawa Za ta Maida Hankali Akan Matsalar Palasdinu
Babban magatakardar Kungiyar Kasashen larabawa ta ce; za ta bada muhimmanci ga kudurorin da su ke da alaka da Palasdinu.
Babban magatakardar Kungiyar Kasashen larabawa ta ce; za ta bada muhimmanci ga kudurorin da su ke da alaka da Palasdinu.
A wata hira da tashar telbijin din Sky News ta larabci ta yi da babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen larabawan, Ahmad Abul-Gaidh, ya ci gaba da cewa; Samar da fahimtar juna da sulhu a tsakanin kungiyoyin palasdinawa wani abu ne da ya zama wajibi. Bugu da kari, babban magatakardar kungiyar ta kasashen larabawa ya yi ishara da halin da ake ciki a kasar Libya sannan ya ce; Kungiyar tana mu'amala da dukkanin kungiyoyin da su ke a cikin kasar.
Kungiyar kasashen larabawa tana yin taronta karo na 28 ne a yankin Bahrul-Mayyit da ke kasar Jordan.