Taron Shugabannin Kasashen Larabawa Da Gagarumin Sabanin Da Ke Tsakaninsu
(last modified Fri, 31 Mar 2017 06:08:45 GMT )
Mar 31, 2017 06:08 UTC
  • Taron Shugabannin Kasashen Larabawa Da Gagarumin Sabanin Da Ke Tsakaninsu

A shekaran jiya Laraba, 29 ga watan Maris, 2017 ce aka kawo karshen taron shugabannin kasashen kungiyar hadin kan kasashen larabawa karo na 28 a yankin Bahrul Mayyit na kasar Jordan inda babban sakataren kungiyar ya karanto sanarwar bayan taro da ke nuni da gagarumin sabanin da ke tsakanin shugabannin larabawan.

Shi dai wannan taron na kwana guda wanda aka gudanar da shi karkashin jagorancin Sarkin Jordan Abdullahi na biyu wanda ya karbi shugabancin kungiyar daga wajen shugaban kasar Mauritaniyya, ya sami halartar da dama daga cikin shugabannin kasashen larabawan. A sanarwar bayan taron da aka fitar an yi ishara da batutuwa irin su rikicin kasar Siriya, Iraki da Palastinu bugu da kari kan mu'amala da haramtacciyar kasar Isra'ila. Babban abin da sanarwar bayan taron take nuni da shi, shi ne gagarumin karo da juna da ke cikin abin da shugabannin larabawan suke fadi da kuma abubuwan da suke aikatawa a aikace.

A halin da ake ciki dai, a fili yake cewa, mafi muhimmanci da girman rikicin da ke faruwa a duniya na faruwa a kasashen larabawan. Ko shakka babu batutuwa irin su rikicin kasashen Siriya, Iraki, Yemen, Libiya da Sudan bugu da kari kan ayyukan ta'addanci da yakin basasa su ne a kan gaba cikin rikice-rikicen da duniya take fuskanta a halin yanzu. Don kuwa kowane guda daga cikin wadannan lamurra aka duba za a ga cewa a kan kansa ya ishi ya zama wata barazana da kuma kalubale ga tsaro da zaman lafiya duniya, don ko ba komai sun haifar da matsalar 'yan gudun hijira ga kasashen duniyan.

To amma abin bakin cikin shi ne cewa duk da irin wannan yanayin cibiyoyin kasashen larabawan ciki kuwa har da kungiyar hadin kan kasashen larabawan sun gagara samun nasarar dakatar da ko da guda daga cikin wadannan matsalolin. Akwai dalilai masu yawa na wannan rashin nasara, wanda daya daga cikin mafi girma da muhimmancin wadannan dalilai shi ne irin rawar da manyan kasashen wannan kungiyar suke takawa.

A matsayin misali, a karshen wannan taron na larabawa, an bayyana cewar hanya guda kawai ta magance rikicin kasar Siriya ita ce hanya ta siyasa. To amma a fili yake cewa daya daga cikin manyan abubuwan da suke hana cimma sulhu a kasar Siriyan shi ne irin goyon bayan da wadannan manyan kasashen na larabawa musamman kasar Saudiyya suke ba wa kungiyoyin 'yan ta'adda da suke yaki a Siriyan da kuma kokarin wadannan shugabannin na kifar da gwamnatin Siriyan. Haka nan dangane da rikicin kasar Iraki ma, shugabannin larabawan sun bayyana wajibcin goyon bayan gwamnatin Irakin a fadar da take da ta'addanci, a daidai lokacin da a lokuta da dama jami'an gwamnatin Irakin sun sha bayyana cewar wasu daga cikin manyan kasashen larabawan su ne kan gaba wajen goyon bayan 'yan ta'addan kungiyar Da'esh a Irakin.

Har ila yau kuma a sanarwar bayan taron, an yi ishara da batun hakkokin al'ummar Palastinu musamman ma hakkin ayyana makoma da kuma kafa kasar Palastinu mai cin gashin kanta, to amma a bangare guda wasu daga cikin shugabannin larabawan su ne kan gaba cikin neman tafiya tare da haramtacciyar kasar Isra'ila da kuma kokarin biya mata bukatunta.

Dukkanin wadannan dalilai da ma wasunsu lamurra ne da suke nuni da cewa kungiyar hadin kan kasashen larabawan ta gaza wajen cimma wani abin a zo a gani, sannan kuma sun sake tabbatar da abin da wasu masana da ma mafi yawa daga cikin al'ummomin kasashen larabawan suka jima suna fadi na cewa taron shugabannin kasashen larabawan bai wuce kawai wani taro na tattaunawa da fitar da sanarwar bayan taro kawai ba.