Masar : Kotu Ta Ce A Baiwa Saudiyya Tsibirai
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i19084-masar_kotu_ta_ce_a_baiwa_saudiyya_tsibirai
Wata kotu a Masar ta ce hukuncin kin mallakwa Saudiyya wasu tsibirai biyu dake a Bahar Maliya bai halasta ba.
(last modified 2018-08-22T06:59:54+00:00 )
Apr 03, 2017 06:29 UTC
  • Masar : Kotu Ta Ce A Baiwa Saudiyya Tsibirai

Wata kotu a Masar ta ce hukuncin kin mallakwa Saudiyya wasu tsibirai biyu dake a Bahar Maliya bai halasta ba.

A watan Janairun wannan shekara ce wata kotu ta yi watsi da yunkurin shugaba Abdel fatah Al'Sisi na mikawa Saudiyya tsibiran biyu da babu mutanen dake rayiwa a ciki.

Batun ya jayo kace -nace da kuma zanga-zanga da tofin Allah tsine na wasu Misrawa.

Idan dai har hakan ta tabbata to mai yiwa ta maido da boren da aka fuskanta a wannan kasar kan batun na mikawa Saudiyya tsibiran na Tiran da Sanafir, koda yake akwai yiwuwar a kara daukaka kara a kan hukuncin na baya-bayan nan, sannan dole a karshe, sai majalisar dokokin Masar din ta amince kafin a mika tsibiran ga Saudiyya.

Dangantaka tsakanin kasashen biyu ta dan farfado a baya bayan nan inda ake sa ran Al'Sissi zai ziyarci kasar ta Saudiyya a cikin wannan watan.