Dangantaka Na Kara Tsami Tsakanin Amurka Da Kawayen Syria
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i19290-dangantaka_na_kara_tsami_tsakanin_amurka_da_kawayen_syria
Dangantaka na kara tsami tsakanin Amurka da kasashen dake goyan bayan gwamnatin shugaba Bashar Al'Assad na Syria, tun bayan harin makami masu linzamin da Amurka ta kaiwa Syriar a wannan makaon mai karewa.
(last modified 2018-08-22T11:29:56+00:00 )
Apr 09, 2017 16:51 UTC
  • Dangantaka Na Kara Tsami Tsakanin Amurka Da Kawayen Syria

Dangantaka na kara tsami tsakanin Amurka da kasashen dake goyan bayan gwamnatin shugaba Bashar Al'Assad na Syria, tun bayan harin makami masu linzamin da Amurka ta kaiwa Syriar a wannan makaon mai karewa.

Wannan dai na zuwa ne bayan da AMurka ta bukaci kawo karshen mulkin shugaban Bashar Al'Assad da kuma kasashen dake rufa masa baya da suka hada da Rasha da Iran wadanda suka sha alwashin maida wa AMurka martani kan wannan harin.

Kamar yadda jakadiyyar Amurka a MDD,  Nikki Haley ta bayyana a gidan talabijin din CNN, ta ce babu wata mafita siyasa a yanzu muddun dai shugaba Assad na kan mulki.

Ta kara da cewa ganin bayan gwamnatin Assad shi ne kawai matakin da zai zo, sai kuma yaki da 'yan ta'addan IS da kuma danawa Iran birki akan tasirin da take dashi a yankin.

Saidai wata sanarwa da kawance da ya hada kasashen Rasha, Iran da Syria da kuma kungiyar Hezbollah ta kasar Lebonan ya ce zai maida martani mai tsanani kan duk wani yunkuri na kaiwa Syria hari da kuma sabawa jan layin da suka shata.