An Bukaci Taimakon Red Cross Kan Yajin Cin Abincin Fursunonin Palastinawa
(last modified Sat, 22 Apr 2017 17:34:49 GMT )
Apr 22, 2017 17:34 UTC
  • An Bukaci Taimakon Red Cross Kan Yajin Cin Abincin Fursunonin Palastinawa

An bukaci kungiyar bayar da agajin gaggawa ta duniya Red Cross da ta taimaka wajen ganin an warware batun yajin cin abinci da fursunonin Palastinawa ke yi.

Jakadan Palastinu a majalisar dinkin duniya Riyadh Mansur ya bayyana cewa, akwai bukatar kungiyar Red Cross da ta taimaka wajen ganin an warware batun yajin cin abinci da Palastinawa ‘yan kaso ke yi, saboda halin da suke ciki yana da matukar hadari.

Yanzu haka daikimanin palastinawa 1500 da ke gidan kason haramtacciyar kasar Isra’ila ne suka shiga yajin cin abinci, bayan kiran da Marwan Bargusi kusa a kungiyar Fatah ya yi, wanda shi ma ake tsare da shi tsawon shekaru a gidan kason Isra’ila, domin nuna rashin amincewa da halin kunci da suke ciki a wuraren da ake tsare da su.

A lokutan baya ma wasu daga cikin Palastinawan da Isra’ila ke tsare da su sun yi yajin cin abinci, domin neman wasu bukatunsu daga haramtacciyar kasar Isra’ila dangane da tsare su da ake yi bisa zalunci, wanda kuma ta hanyar hakan sun cimma burinsu.