Jawabin Shugaban Kungiyar Hizbullah kan muhimiyar rawar da gwagwara ke taka
(last modified Sun, 06 Mar 2016 17:39:00 GMT )
Mar 06, 2016 17:39 UTC
  • Jawabin Shugaban Kungiyar Hizbullah kan  muhimiyar rawar da gwagwara ke taka

Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lobnon ya tabbatar da cewa ba za su yi jirar kungiyar kasashen Larabawa wajen gwagwarmaya da makiya sahawoniya ba

Yayin taron tunawa da shahadar Ali Ahmad Fayad wanda aka fi sani da Haj Ala daya daga cikin komondojin kungiyar Hizbullah, wanda yayi shahada a yankin Ansar dake kudancin kasar, Sayid Hasan Nasrullah ya gabatar da jawabi a marecen yau inda ya jinjinawa Shahidin da irin gudumuwar da ya bayar wajen yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda a kasashen Siriya da Iraki, bayan haka ya jinjinawa kasashen Iran da Siriya game da irin goyon bayan da suke baiwa gwagwarmaya ,sannan yace Dakarun gwagwarmaya ba sa bukatar izini da kuma goyon bayan kungiyar kasashen Larabawa , Dakarun da kuma makaman kasashen Larabawa wajen yaki da makiyar Sahayonia, da kungiyar Hizbullah ta yi jirar kasashen Larabawa domin kare mutunci da kuma kasar Lobnon, da yanzu Haramcecciyar kasar Isra'ila ta mamaye kasar.

Yayin da yake ishara kan yadda magabatan HKI ke ci gaba da kaskantar da Al'ummar Larabawa ta hanyar wulakantar da Al'ummar Palastinu da kuma yadda suke ci gaba da kai hare-haren a gurare masu tsarki na Al'ummar musulmi , Sayid Hasan Nasrullah ya ce wasu kasashen Larabawa na iya kokarinsu wajen cimma yarjejjeniya domin kare manufofin Haramcecciyar kasar Isra'ila ne, lamarin da ba zai taba cimma nasara ba. kuma kokarin da wasu kasashen Larabawa ke yi na kafa Rundunar hadin gwiwa wani mafarki ne da muke fatan rashin tabbatuwarsa kuma muna fatan yin hakan kadan ba zai kasance wata sabuwa mamaya da kasashen ke son yi ta hanyar Haramcecciyar kasar Isra'ila ba.

yayin da yake ishara kan zakon kasan da wasu kasashen Larabawa ke yiwa kungiyar gwagwarmayar musaman ma kasar Saudiya, Sayid Hasan Nasrullah ya tabbatar da cewa domin ci gaba da rayuwar wadannan kasashe da kuma ci gaba da zama kan karagar milki,sun sanya goyon bayan haramcecciyar kasar Isra'ila a kan gaba.