Tanzaniya : An Kori Ma'aikata 10,000 Saboda Difloma Na Bogi
Apr 29, 2017 06:34 UTC
Shugaba John Magufuli na Tanzaniya ya sallami ma'aikata 10,000 daga bakin aiki saboda amfani da takardun difloma ko na aiki na karya.
Wannan matakin dai ya biyo bayan da wani binciken gwamantin kasar ya bankado dubban ma'aikatan dake aiki da takardun na jabu.
Binciken ya nuna cewa wasu ma'aikatan na amfani da takardun 'yan uwansu yayin da wasu takardun kuma na jabu ne.
Tuni dai shugaban kasar ya bada umurnin korar ma'aikatan bayan an bukace su dasuyi murabus ba tare da wata-wata ba, tare kuma da hana su albashin watan Afrilun nan.
Tags