An Hallaka Daya Daga Cikin Kwamandojin IS A Kudancin Damascus
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i20292-an_hallaka_daya_daga_cikin_kwamandojin_is_a_kudancin_damascus
Daya daga Komondojin Kungiyar IS ya hallaka a kudancin birnin Damascus fadar mulkin kasar Siriya
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
May 11, 2017 14:47 UTC
  • An Hallaka Daya Daga Cikin Kwamandojin IS A Kudancin Damascus

Daya daga Komondojin Kungiyar IS ya hallaka a kudancin birnin Damascus fadar mulkin kasar Siriya

Kamfanin dillancin labaran Irna na kasar Iran ya nakalto wata majiya ta kusa da 'yan tawayen Siriya a wannan Alkhamis na cewa an bindige Faras Ganim wanda aka fi sani da Abu Maryam a kusa da wani wuri da ake kira da Hajaril-Aswad dake kudancin birnin Damuscus fadar milkin kasar Siriya.kafin hakan dai mayakan 'yan ta'addar ISIS din na zarkin Abu Maryam da rarraba kawunan Dakarun kungiyar.

A bangare guda mayakan 'yan ta'addar ISIS sun hallaka Muhamad Ahmad Al-hariri daya daga cikin manyan Kwamandojin  kungiyar Tahrirul-Sham a tsakiyar sansanin Yarmuk dake kudancin birnin  Damascus.

A nata bangare cibiyar watsa labarai na yakin kasar Siriya ta watsa faifai video kan yadda Dakarun kasar ke ci gaba da samun nasara a kan 'yan ta'addar ISIS a tsibiran Shumariyah dake gefen garin Hums a wannan Alkhamis.a jiya Laraba ma Dakarun tsaron na Siriya sun dakatar da hare-hare a wani yanki na gefen gabashin Hums bayan da suka tsarkake shi daga mamayar 'yan ta'addar ISIS.