Masar: An Gano Makamai A Yankin Sina
(last modified Sun, 14 May 2017 06:40:20 GMT )
May 14, 2017 06:40 UTC
  • Masar: An Gano Makamai A Yankin Sina

Sojojin Kasar Masar sun sanar da gano makamai masu yawa da abubuwa masu fashewa a yankin Sina.

Sojojin Kasar Masar sun   sanar da gano makamai masu yawa da abubuwa masu fashewa a yankin Sina.

Kamfanin Dillancin Labarun Anatoli na kasar Turkiya, ya ambato kakakin sojan Masar, Tamir Rufa'i yana fadin cewa; dakarun tsaron kasar sun kai hari a tsakiyar yankin Sina, inda su ka yi nasarar gano makamai masu yawa da abubuwa masu fashewa.

Tamir Rufa'i ya jaddada cewa; Dakarun tsaron kasar sun kuma yin samu bama-bamai da aka riga aka shirya su domin fashewa, kamar kuma yadda su ka kame mutane uku.

A gefe daya, da marecen ranar juma'a sojojin na Masar sun kashe 'yan ta'adda 8 a yankin na Sina.

Yankin Sina ya zama wata cibiya da kungiyoyin 'yan ta'adda su ke kai wa sassa daban-daban na Masar hari, tun a 2014.