Trump Da Salman Sun Ce Iran Ce Tushen Ta'addanci Na Duniya
(last modified Sun, 21 May 2017 17:20:25 GMT )
May 21, 2017 17:20 UTC
  • Trump Da Salman Sun Ce Iran Ce Tushen Ta'addanci Na Duniya

A taron da masarautar Saudiyyah ta shirya wa Donald Trump a birnin Riyadh wanda aka gayyaci wasu shugabannin kasashen larabawa da wasu na musulmi, sarkin masarautar Al Saud Salman bin Abdulaziz tare da babban bakonsa Donald Trump, sun dora alhakin dukkanin ayyukan ta'addancin da ke faruwa a duniya a kan kasar Iran.

Trump da Salman har suka gama jawabin nasu ba su ambaci A jawabin da sarki Salman ya gabatar, ya nuna matukar muhimmancin hada karfi da karfe a tsakanin kasashen larabawa da Amurka domin tunkarar abin da ya kira barazanar Iran, inda ya ce ita ce tushen duk wani ta'addanci a duniya.

Shi ma a nasa bangaren Donald ya karfafa abin da sarkin na Saudiyya ya fada, inda ya ce Iran ce take daukar nauyin kungiyoyin 'yan ta'adda a Syria da Iraki Lebanon Yemen da sauransu, tare da jaddada cewa Amurka za ta hada kai tare da Saudiyya da sauran kawayenta larabawa da ma kasashen musulmi domin tunkarar Iran.

Haka nan kuma Trump ya jinjina wa kasashen larabawan yankin tekun Fasha irin su hadaddiyar daular larabawa da Bahrain, wadanda ya kira su da abokan Amurka.

Amurka ta kulla cinikin mamakai tsakaninta da kasashen larabawan yankin tekun fasha na biliyoyin daloli a cikin 'yan watannin da suka gabata, inda a jiya ma ta kulla wani cinikin wasu makamai da za ta sayarwa gwamnatin Saudiyya na dala biliyan 110.

Trump da Salman har suka gama jawabin nasu ba su ambaci sunayen kungiyoyin 'yan ta'addan da Iran ta kafa ko take daukar nauyinsu ba, duk kuwa da cewa kungiyoyin 'yan ta'addan wahabiyya takfiriyyah da suka addabi duniya kowa ya sansu da inda akidarsu ta samo asali.