Turkiyya : An Fara Shari'ar Wadanda Ake Tuhuma Da Juyin Mulki
(last modified Mon, 22 May 2017 13:19:54 GMT )
May 22, 2017 13:19 UTC
  • Turkiyya : An Fara Shari'ar Wadanda Ake Tuhuma Da Juyin Mulki

A Turkiyya an fara shari'a wasu mutane sama da 200 da ake zargi da hannu a yunkurin kifar da gwamnatin shugaba Recep Tayyip Erdogan a cikin watan Yuli 2015.

Mutanen 221 da akewa wannan tuhumar sun hada da babban malamin nan na kasar Fetullah Gullen dake gudun hijira a Amurka, da kuma wasu janar-janar 26.

Sauren laifukan da ake tuhumar mutanen dasu sun hada da sabawa kundin tsarin mulki, da kisan mutane 250 da kuma alaka da kungiyar 'yan ta'adda.

Ana dai gudanar da shari'ar ce a gidan yarin Sinkan dake kusa da birnin Ankara cikin kwararen matakai na tsaro.