IS Ta Dauki Alhakin Kai Hari Kan Kifdawa A Masar
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i20774-is_ta_dauki_alhakin_kai_hari_kan_kifdawa_a_masar
Kungiyar 'yan ta'adda ta IS ta ce ita keda alhakin kai harin da ya yi sanadin mutuwar Kristocin Kifdawa 29 a birnin Minya dake tsakiyar kasar Masar.
(last modified 2018-08-22T07:00:10+00:00 )
May 27, 2017 09:36 UTC
  • IS Ta Dauki Alhakin Kai Hari Kan Kifdawa A Masar

Kungiyar 'yan ta'adda ta IS ta ce ita keda alhakin kai harin da ya yi sanadin mutuwar Kristocin Kifdawa 29 a birnin Minya dake tsakiyar kasar Masar.

Wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta shafin intanet din ta na Amaq ta ce wasu mayakan ta ne suka kai kan motar fasinja a jiya Juma'a.

Alkalumen da ma'aikatar cikin gidan kasar Masar ta fitar dai sun nuna cewa mutane 29 ne suka mutu a harin ciki har da yara.

A cewar sanarwar mutanen rufe da fuskoki dauke da nakamai cikin motoci kirar pick-up sun buda wuta kan motar dake daukeda fasinjojin kafin daga bisani su arce.

Reshen kungiyar IS a kasar Masar dai ya jima yana kai hari kan Kristoci kifdawa.

Ko a watan Afrilu daya gabata ma kungiyar ta IS ta dauki alhakin kai hari kan wasu coci biyu na kifdawa a kasar ta Masar wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 45, bayan wani harin kunar bakin wake a wata coci a tsakiyar birnin Alkahira wanda yayi sanadin mutuwar mutane 29 a watan Disamba.

Bayan hakan ne shugaba Abdel Fatah Al-sisi ya ayyana dokar ta baci ta wattani uku da kuma zargin 'yan jihadin da neman raba kan al'umma.