Jami'an Tsaron Saudiya Sun Kai Hari Kan Dan Uwan Sheikh Nimr
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i21254-jami'an_tsaron_saudiya_sun_kai_hari_kan_dan_uwan_sheikh_nimr
A ci gaba da ta'addancin Saudiya kan mabiya mazhabar Shi'a, Jami'an tsaron kasar sun kai hari kan Dan Uwan Shekh Shahid Bakir Nimr a garin Awamiya.
(last modified 2018-08-22T11:30:14+00:00 )
Jun 12, 2017 11:21 UTC
  • Jami'an Tsaron Saudiya Sun Kai Hari Kan Dan Uwan Sheikh Nimr

A ci gaba da ta'addancin Saudiya kan mabiya mazhabar Shi'a, Jami'an tsaron kasar sun kai hari kan Dan Uwan Shekh Shahid Bakir Nimr a garin Awamiya.

Kamfanin dillancin labaran Pars ya habarta cewa Jami'an tsaron kasar Saudiya sun kai hari kan Muhamad Bakir Nimr Dan Siyasa kuma Dan Uwan Shekh Shahid Bakir Nimr a garin Awamiya inda suka jikkata shi a kafa, kuma yanzu haka yana kwance a Asibitin tsakiyar birnin Qatib yana karbar jiya.

A watan Janirun 2016 ne magabatan kasar Saudiya suka kirkiro tuhuma a kan babban malamin nan  Shekh Nimr Bakir Annimr tare da yanke hukunci kisa gami da  zartar da shi a kansa, a cikin 'yan watanin nan kauyen Almasurat da ya kasance ma'aifar Shekh Nimr Bakir Annimr ya zama wani yanki na ci gaba da gwagwarmayar mabiyar mazhabar iyalan gidan Anabta tsarkaka a gabashin Saudiya.