Masar : Majalisa Ta Amince A Baiwa Saudiya Tsibirai
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i21316-masar_majalisa_ta_amince_a_baiwa_saudiya_tsibirai
Majalisar dokoki a Masar ta amunce da bukatar gwamnatin kasar na mallakawa Saudiya tsibiran nan biyu, Tiran da Sanafir da aka dade ana takkadama akansu a wannan kasa ta Masar.
(last modified 2018-08-22T07:00:15+00:00 )
Jun 14, 2017 10:49 UTC
  • Masar : Majalisa Ta Amince A Baiwa Saudiya Tsibirai

Majalisar dokoki a Masar ta amunce da bukatar gwamnatin kasar na mallakawa Saudiya tsibiran nan biyu, Tiran da Sanafir da aka dade ana takkadama akansu a wannan kasa ta Masar.

Yanzu ya rage ga shugaban kasar Abdel Fattah al-Sissi, wanda ke ci gaba da shan suka kan batun ya rattaba hannu akan kudirin, duk da cewa batun yana gaban kotun tsarin mulkin kasar.

An dai jima ana ta kai kawo gaban kotunan kasar kan batun, inda daga karshe dai wata kotu a birnin Alkahira ta halasta matakin.

An dai kwashe kwanaki uku ana tafka zazzafar muhawara a majalisar dokokin kasar kan wannan batun, wanda a yayinsa 'yan majalisa na bangaren adawa suka sha uhu na kalubalantar matakin.

A watan Afrilu na 2016 ne shugaba Abdel fatah Al-sisi ya mallakawa Saudiya tsibiran biyu na Tiran da Sanafir dake Bahar Maliya, matakin da Misrawa suka yi ta Allah Wadai da shi.