An Bukaci Sojojin Qatar Su Fice Daga Bahrain
Kasar Bahrain ta bukaci sojojin kasar Qatar dake cikin kawacen kasa da kasa dake yaki da kungiyar IS dasu fice daga kasar a cikin sa'o'i 48 masu zuwa.
Wata majiya mai tushe ta shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa mahukuntan Bahrain sun bukaci babban kwamadan rindinar ta ( Navcent) da Amurka ke jagoranta mai sansani a Bahrain, daya umurci sojojin dasu fice daga kasar a cikin kwanaki biyu.
Babu dai karin haske akan yawan dakarun na Qatar a cikin rindinar, amman dai an ce basu da yawa.
Tun a cikin shekra 2014 ne sojojin na kasar Qatar ke cikin kawacen dake yaki da kungiyar IS a kasashen Iraki, Syria da kuma Afghanistan.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin diflomatsiya na tsakanin Qatar da makoftanta na yankin tekun Pasha ke kara tsami.
Kasashen da suka hada Saudiyya, Hadaddiyar daular Larabawa Bahrain da kuma Masar sun kashe duk wata irin hulda da Qatar bisa zarginta da taimakawa ayyukan ta'addanci, batun da mahukuntan Doha ke ci gaba da musuntawa.