Iraki : IS Ta Wargaza Masallacin Al-Nouri Da Hasumiyar Mosul
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i21558-iraki_is_ta_wargaza_masallacin_al_nouri_da_hasumiyar_mosul
Rindinar sojin Iraki ta ce kungiyar 'yan ta'adda ta IS ta wargaza masallacin Al-Nouri da kuma hasumiyar Mosul mai dadadden tarihi.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Jun 22, 2017 01:57 UTC
  • Iraki : IS Ta Wargaza Masallacin Al-Nouri Da Hasumiyar Mosul

Rindinar sojin Iraki ta ce kungiyar 'yan ta'adda ta IS ta wargaza masallacin Al-Nouri da kuma hasumiyar Mosul mai dadadden tarihi.

Fira ministan Iraki Haidar al'Abadi ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa wargaza wadanan wurare ya nuna cew an yi galaba ne ga yakin da ake da kungiyar IS. 

Saidai a wata sanarwa data fitar ta hanyar shafin yada farfagandanta na amaq, kungiyar ta IS ta musunta wargaza wuraren tana mai dora alhakin hakan ga jiragen yakin Amurka.

Amman kawancen yaki da 'yan ta'addan na IS ya ce kungiyar ta wargaza daya daga cikin mayan wurare masu tarihi na Mosul da Iraki.

Idan ana tune a masallacin na Al-Nouri ne dake Mosul Abou Bakr al-Baghdadi ya ayyana kansa a matsayin Khafika bayan da kungiyar ta IS ta mamaye yankin a cikin shekara 2014.