Sharhi:Dan Karamin Juyin Milki A Saudiya
(last modified Thu, 22 Jun 2017 07:07:54 GMT )
Jun 22, 2017 07:07 UTC

Bayan Sauke Yarima mai jiran gado, Dan Sarkin Saudiya ya zama wanda zai gaji Ma'aifinsa

Tashar Telbijin Al-Arabiya ta sanar da sauke Muhamad bn Na'if Yarima mai jiran gado daga kan mikaminsa tare da maye gurbinsa da Muhamad bn Salman da a yanzu ya zama wanda zai gaji ma'aifinsa.

Kafin hakan dai akwai labaran dake fitowa dangane tsananin sabanin dake a tsakanin 'yan gidan sarautar saudiya, a 'yan kwanaki da suka gabata an bayyana cewa Salman bn Abdul-aziz Sarkin Saudiya na kokarin share fagen dora Dansa Muhamad bn Salman a kan kujerar masarautar Saudiyar,  a cikin 'yan watanin baya-bayan nan  aka kwace mikamai da dama daga hanun Muhamad bn Na'if bn Abdul-Aziz tsohon yarima mai jiran gado.

A ci gaba da canje-canjen Sarkin saudiya, an nada sabin mashawarta guda hudu, biyu daga cikin su, sun fito ne daga gidan Ali-Shekh da su keda danganta da Muhamad Abdul-Wahab wanda ya kirkiro mumunar akidar nan ta wahabiyanci a Duniya.

Wannan canje-canjen dai na zuwa ne a yayin da kasar ta Saudiya ta yanke alakar Diplomasiyar ta kasar Qatar, wannan dai wata dama ce da Sarkin Saudiya ya samu a yayin da ake rikici, ya gaggauta nada Dansa a matsayin wanda zai gaje sa.ko da yake wannan mataki da sarkin Saudiya ya dauka ba ya rasa nasaba da ziyarar da Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya kai birnin Riyad , inda ya baiwa Sarkin Saudiya  cikekken goyon baya kame da kudirin da yake son dauka na sauye-sauye.

Wasu masu Sharhi kan harakokin Siyasa na ganin cewa, manufar Babban tarben da aka yiwa Shugaba Trump na Amurka a birnin Riyad tare kuma da kulla yarjejjeniyar sayan makamai na bilyoyin Daloli shi ne neman amnicewar Shugaban Amurkan game da wannan kudiri da ya dauka na karamin juyin milki.

Yawan gudanar da sauye sauye a Gwamnatin Saudiya cikin 'yan kwanakin nan na a matsayin gagguata kwace madafun ikon kasar daga 'yan uwansa da kuma diyan 'yan uwansa tare da mayar da shi a hanun Dansa,an bayyana cewa  bangarori biyu suka kafa masarautar Saudiya, bangaren Shamry da kuma bangaren Sudairy, Sarakunan shidan da suka yi milkin bayan mutuwar sarki Abdul-Aziz, sun fito ne daga wadannan bangarori guda biyu, uku daga bangaren Shamry, uku kuma daga bangare Sudairy, sarki Salman mai ci yanzu ya fito ne daga bangaren Surairy. kuma a tsakanin wadannan bangarori ne ake gwagwarmayar  neman milki.

Kafin mutuwar sarki Abdul-Aziz din da ya kafa masarautar Saudiya yayi wasicin cewa sarautar gidan ta kasance a tsakanin 'ya'yan sa kafin ta koma ga jikokin sa, kuma matukar 'ya'yan nasa nada rai, kadda a bayar da milki ga jikokin sa.

An kafa masarautar Saudiya ne a shekarar 1932 miladiya.