Jami'an Tsaron Masarautar Saudiyya Sun Tarwatsa Gangamin Ranar Qudus Ta Duniya
(last modified Sat, 24 Jun 2017 11:59:01 GMT )
Jun 24, 2017 11:59 UTC
  • Jami'an Tsaron Masarautar Saudiyya Sun Tarwatsa Gangamin Ranar Qudus Ta Duniya

Jami'an tsaron masarautar Saudiyya dauke da manyan makamai da tankokin yaki sun tarwatsa al'ummar musulmi da suka gudanar da gangami domin raya ranar Qudus ta Duniya a yankin Al-Mansurah da ke garin Awamiyyah na kasar.

Rahotonni sun bayyana cewa: Wasu matasa sun gudanar da taron gangami a yankin Al-Mansurah da ke garin Awamiyyah a lardin Al-Qatif da ke gabashin kasar Saudiyya a jiya Juma'a domin raya ranar Qudus ta Duniya kamar sauran al'ummun duniya da nufin jaddada goyon baya ga al'ummar Palasdinu da ake zalunta, inda tawagar jami'an tsaron masarautar Saudiyya suka farmusu da manyan makamai da rakiyar tankokin yaki, inda suka tarwatsa taron gangamin.

Ranar Juma'ar karshen kowane watan ramadana dai rana ce da al'ummar musulmi gami da 'yantattu daga kowane bangare na duniya suke fitowa domin gudanar da zanga-zangar lumana, taron gangami da gabatar da jawabai kan nuna goyon baya ga al'ummar Palasdinu da suke karkashin bakar siyasar zaluncin yahudawan sahayoniyya 'yan kaka gida.