An Gudanar Da Jerin Gwanon Ranar Quds A Falastinu
Dubun-dubatar Falastinawa sun gudanar da jerin gwanon ranar Quds ta duniya a yankunan daban-daban na Falastinu.
Kamfanin dillancin labaran Irna ya bayar da rahoton cewa, a yau dubun-dubatar Falastinawa sun gudanar da jerin gwanon ranar Quds a yankunan Gaza da kuma gabar yamma da kogin Jordan, inda suka yi ta rera taken 'yancin ga Falastinu da masallacin Quds, tare da yin tir da Allah wadai da mamayar Isra'ila a kan yankunansu, da kuma keta alfarmar wurare masu daraja da yahudawan Isra'ila ke yi.
A birnin Quds ma dubban daruruwan Falastinawa suka halarci sallar Juma'a a yau, duk kuwa da cewa an baza dubban jami'an tsaron yahudawa domin hana gudanar da erin gwanon ranar Quds, tare da hana dubban Falastinawa shiga masalalcin Quds domin salla, sai wadanda shekarunsu suka haura 40.
Duk da wadannan matakan da jami'an tsaron yahudawan suka dauka a birnin Quds, amma dubban musulmi sun yi tarera taken mutuwa ga Isra'ila a cikin harabar masallacin Quds.