Oct 28, 2018 09:13 UTC
  • Hamas: Jinin Shahidan Palasdinawa Ba Zai Taba Tafiya A Banza Ba

Kungiyar ta Hamas ta bakin wani kusa nata Hassan Yusuf ta bayyana cewa; Jinanen Palasdinawan da su ka yi shahada zai zama musabbabin kwato da dukkanin hakkokin palasdinawa.

Cibiyar watsa labaru ta Palasdinawa ta ambato Sheikh Hassan Yusuf  yana bayyana haka ne a wani jawabi da ya yi a wurin jana'izar daya daga cikin shahidan Palasdinawa, Usman Ladaudeh.

Usman Lidaudheh ya yi shahada ne a yayin gangamin da Palasdinawa suke a kowace juma'a domin tabbatar da hakkinsu na komawa gidajensu na gado da aka kore su daga ciki yayin kirkirar harmatacciyar kasar Isra'ila.

An fara gudanar da gangamin ne tun ranar 30 ga watan Maris na wannan shekarar, wanda ya zama taro na kowace juma'a akan iyakar Gaza da Palasdinu da take karkashin mamaya.

Tags