Sojojin Iraki Sun Kwace Ikon Masallacin Al'Nuri Dake Mosul
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i21758-sojojin_iraki_sun_kwace_ikon_masallacin_al'nuri_dake_mosul
Rundinar sojin Iraki ta sanar da kwace daukacin ikon masallacin Al'Nuri dake tsohon garin Mosul daga hannun 'yan ta'adda na IS.
(last modified 2018-08-22T07:00:19+00:00 )
Jun 29, 2017 05:33 UTC
  • Sojojin Iraki Sun Kwace Ikon Masallacin Al'Nuri Dake Mosul

Rundinar sojin Iraki ta sanar da kwace daukacin ikon masallacin Al'Nuri dake tsohon garin Mosul daga hannun 'yan ta'adda na IS.

A watan Yuli na 2014 a cikin masallacin na Mosul ne Abou Bakr al-Baghdadi ya yi wa'azinsa na farko a matsayin jagoran kungiyar  ta IS.

Tunda farko dai wani Kwamandan rundinar ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa dakarun basu kai ga kwace ikon masallacin ba aman suna kan hanyar yin hakan.