Masar Ta Yi Wa Kasar Katar Barazara.
Ministan harkokin wajen kasar Masar Samih Shukri, ya bai wa Katar zabi tsakanin kare tsaron kasashen larabawa ko kuma raunana shi.
Ministan harkokin wajen kasar Masar Samih Shukri, ya bai wa Katar zabi tsakanin kare tsaron kasashen larabawa ko kuma raunana shi.
Shukri ya ci gaba da cewa; kasarsa za ta yi tsayin daka wajen fuskantar ayyukan ta'addanci domin tunbuke shi daga tushe haka nan kuma hanyoyin samun kudaden shigar 'yan ta'adda.
Kaashen Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Masar da Bahrain, sun yanke huldar diplomasiyya da kasar Katar, wacce su ka zarga da taimakawa ta'addanci da wuce gona da iri.
Kasashen sun gindaya sharudda 13 ga kasar ta Katar, matukar tana son su sake maida huldar jakadanci da ita. Daga cikin sharuddan da akwai rufe tashar telbijin din aljazeera da dukkanin cibiyoyin da su ke karkashinta, haka nan kuma rage alakarta ta diplomasiyya da Tehran.
Ma'aikatar harkokin wajen Katar dai ta karyata zarge-zargen da aka yi mata, tare da bayyana sharuddan da aka gindaya mata a matsayin wani yunkuri na raba ta da cin gashin kanta.