Iraki : Ana Daf Da Kawo Karshen IS A Mosul
Wani babban kwamanda a rundinar sojin Iraki ya ce nan da 'yan kwanaki, kasar za ta sanar da kwace daukacin ikon tsohon birnin Mosul daga hannun kungiyar 'yan ta'adda ta IS ko (Da'esh).
Janar Abdel Ghani al-Assadi ya bayyana a wata hira da kamfanin dilancin labaren AFP cewa nan ba da dadewa ba zamu sanar da nasara karshe kan kungiyar Daech.
Janar din ya kara da cewa kimanin mayakan kungiyar ta Daech 200 zuwa 300 galibi 'yan kasashen waje ne suka buya a cikin tsohon garin na Mosul, wanda ke zamen babban sansani kuma na karshe na kungiyar ta IS a Iraki.
Dama kafin hakan wani kwamadan kawancen da Amurka ke jagoranta kan yaki da kungiyar a Mosul ya fada cewa kwato dukkan biranen Iraki daga kungiyar '' batu na dan lokaci''.