Iraki : An Yi Murnar Murkushe IS A Mosul
Sojoji da mazauna tsohon birnin Mosul na Iraki sun yi murnar muskushe kungiyar ‘yan ta’adda ta IS ko kuma Da’esh.
Kafofin yada labarai daga Iraki sun nuna hotunan mazauna birnin da sojoji na ta raye-raye a titunan birnin bayan tsarkake wasu mahimman wurare na tsohon garin.
Kwamada rundina musamen ta Iraki, Janar Nabil al-Fatlawi ya shaidawa masu aiko da rahotanni cewa nan bada dadewa ba za’a sanar da kawo karshen kungiyar.
Saidai ya ce daya daga cikin abunda ke basu wuya a yakin da ake da kungiyar shi ne tsakakiya dake a kwai a wasu lungunan birnin sai kuma garkuwa da fararen hula da kungiyar ke yi a wasu lokaci.
Bayanai daga birnin sun ce mutane sun samu sukuni da kuma kwarya-kwarya zamen lafiya tun lokacin da sojojin kasar suka kaddamar da farmakin karshe kan ‘yan ta’addan na IS a birnin na Mosul