Kasar Katar Ta Mikawa Kuwait Jawabin Bukatun Larabawan Tekun Pasha.
(last modified Tue, 04 Jul 2017 06:48:38 GMT )
Jul 04, 2017 06:48 UTC
  • Kasar Katar Ta Mikawa Kuwait Jawabin Bukatun Larabawan Tekun Pasha.

Ministan harkokin wajen kasar Katar ya ziyarci kasar Kuwait inda ya mika jawabin kasar ga sarki Sabah al-Ahmad.

Ministan harkokin wajen kasar  Katar ya ziyarci kasar Kuwait inda ya mika jawabin kasar ga sarki Sabah al-Ahmad.

Kamfanin dillancin labarun Kuwaiti ( Kona) ya ce; Muhammadu Bin Abdurrahman ali-Sani, tare da tawagar da ta yi masa rakiya, sun gana da sarki Sabah, al-Ahmad ali Sani, inda ya mika masa  rubutaccen jawabin Katar daga Tamim Bin Hamad Bin Khalifa ali-Sani.

Jawabin na kasar Katar ya zo ne bayan da wa'adin da kasashen Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Bahrain da Masar, ya zo karshe na cewa Katar din ta aiwatar da wasu bukatu 13.

Bukatun dai sun kunshi rufe tashar telbijin din aljazeera da dukkanin cibiyoyin da su ke karkashinta da kuma rage alakar diplomasiyya da Iran da korar 'yan Ikhwanul Muslimin da Hamas daga Doha.