Wani Bapalastine Yayi Shahada A Kudancin Baitu-Laham
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i21986-wani_bapalastine_yayi_shahada_a_kudancin_baitu_laham
Wani Matashi Baplastine yayi shahada bayan da wani Bayahude dan kama wuri zaune ya kade shi da Mota a kusa da kauyen Khadar dake kudancin Baitu-Laham na gabar tekun Jodan
(last modified 2018-08-22T11:30:21+00:00 )
Jul 07, 2017 11:16 UTC
  • Wani Bapalastine Yayi Shahada A Kudancin Baitu-Laham

Wani Matashi Baplastine yayi shahada bayan da wani Bayahude dan kama wuri zaune ya kade shi da Mota a kusa da kauyen Khadar dake kudancin Baitu-Laham na gabar tekun Jodan

Cibiyar Kafafen yada Labarai ta yankin Palastinu ta habarta cewa a safiyar wannan juma'a wani Bayahude dan kama wuri zauna ya kade wani matashin Bapalastine mai suna Umar Ahmad Abu Galyun mai shekaru 37 a Duniya wanda kuma yake da dan karamin wurin cin abinci da shan shayi a kauyen Khadar dake kudancin Baitu-Laham, inda aka garzaya da shi zuwa Asibiti, saidai jim kadan da kai shi asibitin rai yayi halinsa.

A ko wata shekara Palastinawa da dama ne suke yi shahada musaman ma kananen yara sanadiyar karewa da mota daga bangaren Yahudawa 'yan kama wuri zauna a yankin Palastinu.