Masar: Ma'aikatan Gwamnati Da Su ke Bacewa Suna Karuwa
wata kungiyar kare hakkin bil'adama ta kasar Masar ta ce; Ana ci gaba da samun karuwar kame ma'aikatan gwamnati da kuma bacewar wasu
Wata kungiyar kare hakkin bil'adama ta kasar Masar ta ce; Ana ci gaba da samun karuwar kame ma'aikatan gwamnati da kuma bacewar wasu.
Jaridar al-kuds al-arabi ta ambato kungiyar kare hakkin bil'adama ta: " al-tansiq li huququl-insan wal hurriyah" tana yin ishara da yadda ake kame mutane da kuma yadda wasu su ke bace wa sama ko kasa, wanda hakan ya ke cin karo dadoka ta 9 ta kare hakkin bil'adama da hakkokin 'yan kasa.
Kungiyar ta ci gaba da cewa; A karkashin dokokin kare hakkin bil'adam bai kamata ace an kame wani dan kasa ba tare da dalili ba ko kuma a haramtawa wasu 'yanci.
Kungiyar ta bukaci gwamnatin kasar Masar da ta daina kame mutane musamman dalibai da hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa.