Palasdinu: 'Yan Sahayoniya Sun Mayar Da Birnin Kudus Zuwa Sansanin Soja
Sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila sun mamaye birnin Kudus domin hana palasdinawa Isa masallacin kudus.
Sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila sun mamaye birnin Kudus mako daya bayan hana palasdinawa yin salla a masallacin kudus.
Tun da safiyar yau ne sojojin yahudawan su ka kafa shinge na karfe a kofar Babul Asbat ta masallacin kudus, kamar kuma yadda su ka mamaye duk wasu hanyoyin da su ke isa zuwa ga masallacin.
Rahotanni daga kudus sun cewa; 'yan sahayoniyar sun girke sojoji 2000 a cikin birnin na Kudus.
Dubban palasdinawa da su ka ki amincewa da su bi ta cikin kofar bincike da 'yan sahayoniyar su ka kafa a bakin masallacin kudus.
A wasu sassa-sassa daban-daban na palasdinu an yi taho mu gama a tsakanin samarin palasdinawa da kuma sojojin sahayoniya.