Kungiyoyin Gwagwarmayar Palastinawa Sun Sha Alwashin Mayar Da Martani Ga Sahyoniyawa
(last modified Sat, 22 Jul 2017 05:48:50 GMT )
Jul 22, 2017 05:48 UTC
  • Kungiyoyin Gwagwarmayar Palastinawa Sun Sha Alwashin Mayar Da Martani Ga Sahyoniyawa

Kungiyoyin gwagwarmayar Palastinawa sun sha alwashin mayar da martani mai kaushin gaske ga haramtacciyar kasar Isra'ila matukar ta ci gaba da keta hurumin masallacin Kudus da take ci gaba da yi cikin 'yan kwanakin nan.

Tashar talabijin din Al-Mayadeen cikin wani rahoto da ta watsa a shafinta na Internet ta bayyana cewar a cikin wata sanarwa da kungiyar Izzudden al-Qassam (bangare soji na kungiyar Hamas), dakarun Qudus da na Tufan, kungiyoyin sun ce matukar dai haramtacciyar kasar Isra'ila ba ta kawo karshen irin cin zarafin masallacin na  Kudus da kuma al'ummar Palastinawa masu kare masallacin da take yi, to kuwa za ta fuskanci gagarumin mayar da martanin da ba ta taba ganin irin sa ba.

Sanarwar ta kara da cewa Masallacin Kudus dai wani jan layi ne da al'ummar musulmi ba za su taba amincewa da wani ya ketare shi. Don haka kungiyoyin suka ce suna ci gaba da sanya ido sosai kan abin da ke faruwa a birnin na Kudus kuma za su mayar da martani a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Sama da mako guda kenan sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suke ci gaba da kawanya wa masallacin na Kudus da hana musulmi salla a cikinsa lamarin da ya haifar da rikici tsakaninsu da masallatan inda ko a jiya wani adadi na  Palastinawan sun yi shahada da kuma samun raunkuna.